Halifar Darikar Tijjaniyya Na Duniya Ya Yi Jan Kunne Kan Gwamutsa Siyasa Da Tijjaniyya

Posted by:Abubakar Dundu

  Shugaban darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Tijjaniyya Nyass (RA) ta bakin shugaban tawagar shugabannin Tijjaniyya da su ka zo daga Kaulaha, ta kasar Senegal, domin halartar Zikirin shekara shekara da a ke gudanarwa a fadar masarautar Kano, tun shekaru 21 da su ka wuce, Sayyadi Mahy Aliyu Cisse, ya yi jan kunne ga ainihin 'yan Darikar Tijjaniyya kan su guji gwamutsa siyasarsu da Darikar.

Ya ce siyasa daban Tijjaniyya daban. Kowannensu zaman kan sa ya ke. Ya tabbatar da cewa "Wannan Gwamna na Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje hadimi ne na wannan Darika ta mu da kuma su 'yan Darikar. Khalifa Sheikh Tijjani Nyass ya yi min umarnin da mu isar da sakonsa na taya murna gare shi na sake dawowa kan karagar mulkin Kano."

Ya kuma nusantar da cewa sama da shekaru 50 da su ka wuce, akwai alaka mai karfi tsakanin masarautar Kano da gidan Tijjaniyya daga Kaulaha. Ya ce "Wannan alaka ta mu ba wai yau ko yanzu ta fara ba. Dadaddiya ce kuma cikin soyayyar Allah da Manzonsa, Muhammad Bin Abdullah, Sallallahu Alaihi Wasallam."

Ya yi wadannan jawaban ne ranar Juma'a da daddare da ya halarci cin abincin dare da gwamna Ganduje ya shiryawa wannan babbar tawaga da ta zo daga Kaulaha wajen Zikirin wannan shekara da a ka gabatar. 

Shi wannan Zikirin shekara shekara din an faro shi ne daga lokacin da Kano, ba fa jihar Kano ba a matsayin jiha, ta kai shekaru dubu daya da kafuwa. Daga wancan lokacin yau shekaru 21 kenan a ka faro wannan aikin ibada na Zikirin shekara shekara. Shekarar da ta wuce a ka yi na 20. Wannan shekarar kuma a ka yi na 21.

Sayyadi Cisse ya jagoranci tawagar wacce take dauke da 'ya'yan Sahibul Waqti, Gausuzzaman, Halifar Sheikh Ahmad Tijjani (RA), Sheikh Ibrahim Bin Abdullah Nyass Al-Kaulahi (RA). A cikin tawagar da akwai Sheikh Shafi Nyass, Sheikh Muhammad Zaynab dan Sheikh Abubakar Surunbai akwai kuma Sheikh Abubakar Sheikh Tijjani Nyass.

Shugaban tawagar ya kara da cewa "Mu a can Kaulaha kullum mun yarda da cewar abinda ya shafi Najeriya, musamman jihar Kano, to mu ma ya shafe mu. Saboda haka zaman lafiya a Kano mu ma zaman lafiya ne a wajen mu. 

Saboda ganin yadda wannan bawan Allah gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ke kula da wannan Darika ta mu da mabiyanta, ya sa a wancan lokacin kafin a yi zabe mu ka dage wajen yi masa addu'ar dawowa kan mulki. Alhamdulillah yau ga shi Allah Ya kawo mu dawowarsa. Mu na kara taya ka murnan samun wannan nasara."

Sayyadi Cisse ya ce "Wannan suna na ka na Khadimul Islam ya cancance ka matuka da gaske. Saboda ganin yadda ka ke ta yin dawainiya wajen ganin samuwar bunkasar wannan addini na Musulunci. Sannan mu na yabawa da kokarin da ka ke yi na hada kawunan Musulmi a wannan jiha mai albarka ta Kano da kuma kasa baki daya."

Ya ce sun shaida daga Halifofin Tijjaniyya na wannan jiha da ma kasa gaba daya, yadda gwamna Ganduje ya ke tiri-tiri da su. Sa'annan ya umarci wadannan Halifofi, musamman wadanda su ke a Kano, da su kara dagewa wajen yi wa jihar addu'a ta kara bunkasa da zaman lafiya. 

Dukkan Halifofin, musamman manyan gidajen Darikar Tijjaniyya da ke Kano, sun halarci wannan liyafar cin abincin dare da aka shiryawa wannan babbar tawaga.

A nasa jawabin gwamna Ganduje godiya ya yi na addu'o'in da ya ce wadannan bayin Allah su na ta yi wa wannan jiha ta Kano, har Allah Ya kara kawo dauki a ka kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce dukkanin ilahirin jagororin Tijjaniyya a jihar Kano su na yin iya na su kokarin wajen ganin an samu tabbatuwar zaman lafiyar jihar da kuma bunkasar tattakin arzikinta gami da ci gaban jihar gaba daya. 

"Kuma in sha Allah ba da dacewa ba zan kawo ziyara ta musamman Kaulaha a kasar Senegal. Kamar yadda Shehi ya fada, dukkan abinda ya faru a Kano tamkar ya faru ne a Kaulaha. Saboda kusancin na mu ya kai matuka. Ya kai ya kawo Alhamdulillah. Mu na kara godiya ta musamman kan irin addu'o'in da a ke mana," in ji gwamna.

Gandujen ya ambaci cewar shi wannan Zikirin shekara da ake yi, ba karamin alheri ya ke kawo wa wannan jiha ba. Ya kara da cewa "Mu na kuma kara godiya da wannan babbar alaka da a ka ci gaba da kullawa tsakaninmu. Wannan ya nuna yadda Allah Ya ke cikin wannan al'amarin na kauna da soyayya cikin Allah, saboda Shi kuma a ka fuskance Shi."